Ta ce kasar Sin tana da kwararru masu yawa da kuma fasahohin nukiliya na zamani, wadanda za su iya amfanawa mambobin hukumar IAEA bisa tsarin hukumar ta IAEA.
Kasar Sin ta gabatar da sabbin kayayyaki ga babban taron IAEA, da nufin bunkasa fasahar nukiliya tare da sauran kasashe mambobin hukumar.
Daraktan hukumar makamashin nukiliyar kasar Sin, Zhang Kejian, ya gabatar da dabarun kasar Sin na yin amfani da makamashin nukiliyar don samar da zaman lafiya a lokacin babban taron.
Ya ce kasar Sin za ta yi kokarin neman cigaban bil adama da na halittu yadda ya kamata, da kuma kara daidai tsarin yin amfani da makamashi. A matsayin makamashi mai tsabta, da makamashi marar gurbata muhalli, amfani da makamashin nukilyar don samar da lantarki wanda hakan zai samar da gagarumin cigaba. (Ahmad)