Paul Biya ya wallafa jiya a shafin Tweeter cewa, yana godewa al'ummar Kamaru dake ciki da wajen kasar, saboda sabunta yakininsu a kan sa. Inda ya ce su hada hannu tare, su tunkari kalubalen dake fuskantarsu, wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da kuma ci gaban kasar.
Dan takarar jam'iyyar CRM Maurice Kamto ne ya zo na biyu da kaso 14.23 na kuri'un, yayin da Joshua Osih na babbar jam'iyyar adawa ta kasar wato SDF ya zo na 3 da kaso 3.35.
'Yan takara 9 ne suka fafata a zaben da aka yi ranar 7 ga watan nan. Kididdigar da aka fitar a hukumance ta nuna cewa, kusan mutane miliyan 3.6 daga cikin miliyan 6.7 da suka yi rejista ne suka kada kuri'a, wanda ya kama kaso 53.85.
Ba a samu fitowar masu zabe sosai ba a yankin dake amfani da harshen Ingilishi, inda Jam'iyyar SDF ta fi farin jinni. Kasa da kaso 10 na wadanda suka yi rejista ne suka kada kuri'a, yayin da ake tsaka da fuskantar barazanar rushe zaben daga kungiyar 'yan aware masu dauke da makamai. (Fa'iza Mustapha)