in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Kamaru ta yi gargadi game da tada rikicin bayan zabe
2018-10-27 16:01:24 cri
Ministan kula da yankuna na Kamaru Paul Atanga Nji, ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani rikicin bayan zabe a kasar ba.

Gargadin na zuwa ne, bayan Maurice Kamto na Jam'iyyar Cameroon Renaissance Movement, wanda ya zo na biyu a zaben, ya yi barazanar shirya zanga zanga, bayan ya yi ikirarin lashe zaben.

A ranar Alhamis ne manajan yakin neman zabensa Paul Eric Kingue, ya sanar da wani shiri na kin amincewa da sakamakon zaben, wanda ke da nufin tara al'ummar kasar su gudanar da gangamin kare kuri'un da suka kada.

Paul Nji ya ce wadancan matakai ba su dace ba, yana mai jadadda cewa Maurice Kamto ba shi da wata rigar kariya.

A ranar Litinin ne majalisar kula da kundin tsarin kasar ta ayyana Shugaban kasar mai ci wato Paul Biya, a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 7 ga wata da kaso 71.28 na kuri'un da aka kada. Ana sa ran zababben shugaban kasar zai yi rantsuwar kama aiki a farkon watan Nuwamba mai kamawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China