in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko fasahar cinikayya za ta ciyar da kasashen duniya gaba?
2018-10-12 19:14:34 cri

A cikin sabon rahoton hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda asusun ba da lamunin duniya wato IMF ya bayar kwanan baya, an bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2018 da ta 2019 za ta ragu zuwa kaso 3.7 cikin dari, amma a watan Afrilun da ya gabata, an yi hasashe cewa, adadin zai karu da kaso 3.9 cikin dari.

Asusun IMF ya bayyana cewa, yanzu kasashen duniya suna fuskantar babban kalubalen rikicin cinikayya, bisa dalilin rashin tabbacin manufofin da ake aiwatarwa. A don haka babbar jami'ar asusun Christine Lagarde, ta yi kira ga shugabannin kasashe daban daban, da su yi hadin gwiwa domin gyara tsarin cinikayya na kasa da kasa, a maimakon lalata shi.

Kafin wannan, mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya bayar da wani jawabi, inda ya zargi kasar Sin kamar yadda yake so, ya kuma bayyana cewa, kasarsa za ta kara karbar harajin kwastan, kan kayayyakin kasar Sin da za ta shigar Amurka, kana ya ce, shugaba Trump ya tabbatar da cewa, idan ba za a iya daddale wata yarjejeniyar adalci mai haifar da moriya tsakanin Amurka da Sin ba, to, Amurkar za ta kara karbar harajin kwastan kan kayayyakin kasar Sin.

Daga hakan, cikin sauki za a iya gano cewa, wace kasa ce ke kawo tasiri ga manufofin da ake aiwatarwa, ko wace kasa ke kawo rikicin cinikayya ga kasa da kasa, ko kuma ko wace kasa ce ke rushe tsarin cinikayya na kasa da kasa. Amma a cikin rahoton, Pence ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne, kasarsa dake karkashin jagorancin shugaba Trump, tana kokarin kiyaye moriyarta. Hakikanin ainihin ma'anarsa ita ce, moriyar Amurka ta fi kome muhimmanci.

Tun bayan da Trump ya hau kan kujerar shugaban kasar Amurka, gwamnatinsa ta rika janye jiki daga yarjejeniyoyin kasa da kasa, misali TPP, da yarjejeniyar dakile matsalar sauyin yanayi ta Paris, da yarjejeniyar makaman nukiliya ta Iran. Ta kuma fice daga hukumar UNESCO, da hukumar kiyaye hakkin bil Adama ta MDD da sauransu. Har ma ta yi kalubalen cewa, za ta janye jiki daga hukumar cinikin duniya da kuma MDD.

Kowa ya sani, dole ne a cika alkawarin da aka dauka, amma Amurka ba haka take ba. Wani abun tambayar shi ne, ko Pence yana son a amince da manufar da ya nuna a cikin rahotonsa, cewa wai jagorancin Amurka zai ciyar da duniya gaba?

Amma ba zai yiyu ba a amince da wata kasa wadda ba ta cika alkawarinta ba, haka kuma ba zai yiyu ba a amince da cewa, Amurka za ta ciyar da duniya gaba kamar yadda ta bayyana, idan ba ta gyara kuskuren ta ba, kuma, za ta shiga mawuyancin hali, har ta kai ga haifar da matsala ga daukacin kasashen duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China