in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitocin gargajiyar Sin da aka tura Afirka sun zarta 2000
2018-08-19 16:08:04 cri

Jiya Asabar shugaban hukumar kula da harkokin likitancin gargajiyar kasar Sin Yu Wenming ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana samarwa kasashen Afirka tallafin hidimar likitancin gargajiyar kasar Sin ta hanyoyi daban daban, kawo yanzu gwamnatin kasar ta tura likitocin gargajiya da sun kai sama da 2000 zuwa kasashen Afirka.

Jami'in ya bayyana a yayin taron tattaunawar hadin gwiwar likitancin gargajiya tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a wannan rana cewa, gwamnatin kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwar likitancin gargajiya da kasashen Ghana da Tanzaniya da Comoros da Malawi da Habasha da sauransu. Wannan ya nuna cewa, likitancin gargajiyar kasar Sin yana taka muhimmiyar rawa a aikin kiyaye kiwon lafiyar al'ummun kasashen Afirka, musamman ma wajen rigakafi da magance manyan cututtuka masu saurin yaduwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China