in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Najeriya ta yi Allah wadai da kashe kashe a jihar Plateau
2018-07-04 10:03:16 cri

Majalisar wakilan Najeriya ta yi Allah wadai da kashe rayukan sama da mutane 200 a kwanakin baya a jihar Plateau dake tsakiyar Najeriya, inda ake zargin Fulani makiyaya suka yi, ta bayyana lamarin da cewa rashin imani ne da ta'addanci.

Istifanus Gyang, dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar, wanda ya gabatar da kuduri a zauren majalisar kan lamarin domin daukar matakan gaggawa, ya ce, baya ga hallaka mutanen, an kuma kone kauyuka 52, inda aka kaddamar da hare haren.

Da yake goyon bayan kudurin, shugaban masu rinjaye a majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce lamarin ya wuce batun kabilanci ko kuma bangaren da ake danganta faruwar lamarin da shi, don haka ya bukaci a dauki matakan kawo karshen matsalar.

Bayan tafka mahawara, majalisar ta ayyana kashe kashen a matsayin kisan kiyashi, kana ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki kwararan matakai domin dakile matsalar da kuma tabbatar da tsaron yankunan da ake fama da hare haren.

Majalisar ta shawarci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya dauki matakai a aikace domin kawo karshen matsalar kamar yadda dokar kundin tsarin mulki ta tabbatar.

Hukumomin 'yan sanda sun sanar da cewa, mutane 86 ne suka mutu a sakamakon hare haren a kauyukan jihar Plateau dake tsakiyar Najeriya a ranar 23 ga watan Yuni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China