in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban AU ya bukaci a gudanar da gamayyar kasa da kasa karkashin tsarin MDD
2018-10-25 10:37:56 cri

Mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Afrika (AU) Thomas Kwesi Quartey, ya yi kira ga al'ummar kasashen duniya da su tabbatar da karfafa huldar gamayyar kasa da kasa karkashin inuwar MDD.

Quartey, ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ranar MDD ta bana wadda aka kafa ta tun a shekarar 1945.

Mataimakin shugaban, wanda ya bayyana ranar ta MDD da cewa, rana ce da ba za'a taba mantawa da ita ba, wacce ta dace a ci gaba da bikin tunawa da ita, sai dai ya nuna rashin jin dadi sakamakon yadda wasu manyan kasashen da suka ci gaba suke kawo cikas ga ayyukan MDD da wasu hukumomi na musamman na MDDr.

"Dokokin kasa da kasa wadanda gamayyar kasa da kasa ya kamata su daga matsayinsu suna fuskantar matsin lamba daga wasu manya manyan kasashen duniya." in ji shi.

Quartey ya nanata cewa, Afrika a shirye take ta tabbatar da mutunta dokokin kasa da kasa, wadanda za su tabbatar da daga martabar rawar da kowane bangare na duniya zai taka a harkokin kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China