in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da MDD za su yi hadin gwiwa don kafa tsarin inshora
2018-01-31 11:00:25 cri

Hukumar auna yanayin hasara ta Afrika (ARC), karkashin kungiyar tarayyar Afrika (AU), da hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), sun sanar da aniyarsu ta yin sabuwar hadin gwiwa game da tsarin inshora saboda barazanar matsalolin sauyin yanayi a kasashen Afrika.

Yarjejeniyar ta ARC da ECA, ta kunshi kafa tsarin inshora ne a mambobin kasashen 33, ta yadda za'a zuba jari don samar da kariya game da tsare tsaren ci gaban gwamnatocin kasashen, kamar yadda jami'in ECA ya tabbatar da hakan.

ARC da ECA, za su dinga yin musayar kwararru da kuma samar da kudade don yin aikin hadin gwiwa na bincike game da kididdiga a fannonin tattalin arziki da barazanar sauyin yanayi.

MDD ta yi kiyasin cewa, Afrika za ta iya kashe dala biliyan 50 a duk shekara kan batun sauyin yanayi nan da shekarar 2050.

Mohamed Beavogui, darakta janar na ARC ya ce, sabuwar hadin gwiwar za ta kara karfafa mu'amala tsakanin bangarorin biyu wajen kawar da illolin da sauyin yanayi zai iya haddasawa a Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China