in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi Allah wadai da jingine tattaunawar Comoros
2018-10-18 13:35:00 cri

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da datakar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin siyasar kasar Comoros.

Faki ya yi wannan kiran ne a yayin da bangarorin masu shiga tsakani kan warware dakaddamar siyasar kasar Comoros wanda ya fara aikinsa a ranar 14 ga watan Satumba, wanda babban wakilin AU Ramtane Lamamra, ya yi watsi da shi a ranar 2 ga watan Oktoba, kamar yadda kungiyar AU ta sanar a jiya Laraba.

A ranar Talata MDD ta sake bayyana damuwarta game da rahoton dake nuna cewa, ana ci gaba da samun zaman tankiya a tsibirin Anjouan, yanki mai cin gashin kansa dake tekun Indiya wanda ya shafi wani bangare na kasar Comoros, kana ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa don samun dawwamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Comoros.

A cerwar AU, an samu tabarbarewar al'amurran siyasa a tsibirin ne saboda wasu matakai da aka dauka, musamman saboda janye takunkumin da aka yiwa wasu mambobin majalisar dokoki uku 'yan bangaren adawa a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Mambobin majalisar uku na bangaren adawa, wadanda aka dage musu takunkumin a ranar 3 ga watan Oktoba, suna daga cikin wakilan dake halartar taron tattauna zaman lafiyar kasar.

Faki ya jaddada muhimmancin gaggauta dawowa teburin tattaunawar zaman lafiyar bangarorin siyasar kasar Comoros bisa gaskiya da kyakkyawar fata ga zaman lafiyar kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China