in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sassauta dokar hana fita a jihar Kaduna dake Najeriya
2018-10-25 09:33:40 cri

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, Nasir el-Rufai, a jiya Laraba ya bayyana cewa, an sassauta dokar hana fita da aka saka a babban birnin jihar da kewaye na sa'o'i 24 bayan barkewar tashin hankalin da aka samu a jihar wanda ya yi sanadiyyar rayukan jama'a.

A halin yanzu, an sassauta dokar daga karfe 6 na safe zuwa karfe 5 na yamma, agogon wurin har sai abin da hali ya yi, gwamnan ya fada cikin wata sanarwa da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas.

Gwamnan ya ce, mazauna jihar za su iya fita don gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum, matakin ya biyo bayan matsayar da gwamnatin jihar ta cimma ne bayan taron tattaunawar majalisar zartaswar jihar da hukumomin tsaron da gwamnatin ta kafa wanda aka gudanar a jiya Laraba.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fitar ne a ranar Lahadi, bayan barkewar tashin hankalin da aka samu a babban birnin jihar.

A ranar Talata, gwamnatin ta sanar da ba da damar zirga zirga na tsawon sa'o'i 4 wato daga karfe 1 zuwa 5 na yamma, domin baiwa mazauna birnin damar neman abin bukatunsu, sai dai dokar za ta ci gaba da aiki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China