Wakiliyar musammam ta MDD kan harkokin yara da rikice-rikice Virginia Gamba, ta yi maraba da ceto yara 833 da 'yan sintiri suka yi jiya Juma'a a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.
Virginia Gamba, ta ce wannan muhimmin ci gaba ne ga yara maza da mata a yankin arewa maso gabashin kasar, wadanda rikici da rashin tsaro ya yi mummunan tasiri ga rayuwarsu.
Ta ce, ceto yaran da 'yan sintirin Civilian JTF suka yi, sakamako ne na aikin da suka shafe watanni suna yi bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu da rundunar hadin gwiwa ta MDD dake Nijeriya.
Hukumomi a Nijeriya za su samar da shirye-shiryen sake shigar da su cikin al'umma, da taimakon asusun yara na MDD da abokan huldarsa.
Yayin da ceton yaran ke zaman muhimmiyar nasara ga ba su kariya a Nijeriya, ta jadadda damuwarta game da yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da take hakkokin yara a yankin arewa maso gabashin kasar. (Fa'iza Mustapha)