in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya bukaci a ci gaba da bautawa MDD
2018-10-24 15:56:53 cri

Yau ranar 24 ga watan Oktoba rana ce ta majalisar dinkin duniya, a don haka babban sakataren majalisar Antonio Guterres ya gabatar da wani hoton bidiyo a jiya, inda ya bukaci daukacin al'ummomin kasashen duniya wadanda ke bautawa majalisar da su ci gaba da nuna kwazo da himma domin dakile kalubalen dake gabansu, sannan kada su yi kasa a gwiwa har abada.

Guterres ya sake jaddada cewa, MDD tana da niyyar dakile matsalar sauyin yanayi, da kiyaye hakkin bil Adama tare kuma da wanzar da zaman lafiya a fadin duniya.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata a dauki alkawari tare a wannan rana mai ma'ana wato sake aminta da juna domin ceton duniya, sannan a hada hannu a tafi tare, kana a rika mutunta juna a MDD.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China