in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: CAR tana da tushen wanzar da zaman lafiya
2018-10-24 11:14:12 cri

Manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya CAR Parfait Onanga-Anyanga ya bayyana cewa, kawo yanzu kasar ta riga ta mallaki tushen wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Yayin da yake bayani kan yanayin da kasar Afirka ta Tsakiya ke ciki ga kwamitin sulhun MDD a jiya, Onanga-Anyanga ya bayyana cewa, duk da cewa kasar tana fuskantar kalubale mai tsanani, ta riga ta mallaki wajibabben tushen shimfida dawwamamen zaman lafiya. Ya ce muddin gwamnatin kasar da al'ummarta suka yin kokari tare karkashin goyon bayan kasashen duniya, za su cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa.

Jami'in ya kara da cewa, an riga an shawo kan rikicin siyasar kasar, haka kuma an riga an maido da kundin tsarin mulkin kasar, a don haka gwamnatin na kara tafiyar da harkokin kasar daga duk fannoni.

Amma jami'in ya yi kashedin cewa, akwai yiwuwar aukuwar hargitsi a kasar, inda ya ce wani lokaci a kan kai hari ga fararen hula, shi ya sa al'ummun kasar ke bukatar taimakon jin kai, yana mai kira ga kasa da kasa da su yi kokari tare da gwamnatin kasar domin tabbatar da burin wanzar da zaman lafiya a kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China