in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: MDD za ta yi hadin gwiwa da AU don magance matsalolin Afrika
2018-10-18 13:25:51 cri

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da kungiyar tarayyar Afrika AU wajen warware matsalolin Afrika.

Guterres ya bayyana a lokacin taron tattaunawa game da Afrika na shekarar 2018 wanda aka shirya da nufin zaburar da kasa da kasa wajen tallafawa ci gaban nahiyar Afrika cewa, MDD ta yi amanna cewar shugabancin kasashen Afrika shi ne zai iya warware matsalolin nahiyar, kuma a shirye MDDr take ta yi aiki da kungiyar tarayyar Afrika da ba ta goyon baya da amfani da yawan damammakin da ake da su a halin yanzu.

Jami'in MDD ya ce, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniya watannin 18 da suka gabata game da batun aiwatar da ajandar samar da dawwammman ci gaba nan da shekarar 2030 ,da ajandar raya ci gaban Afrika bisa hadin gwiwar MDD da AU nan da shekarar 2063, da nufin samar da hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya da tsaro wanda bangarorin biyu suka cimma matsaya.

Da yake karin haske game da muhimmancin samar da kudade da aiwatar da ajandodin, babban jami'in MDD ya bukaci dukkanin kasashe su tabbatar da mutunta yarjejeniyar da aka cimma a taron Addis Ababa a shekarar 2015 game da ajandar samar da dawwamaman ci gaba.

An kaddamar da taron tattaunawar na Afrika na wuni biyu a ranar Laraba wanda ofishin musamman kan harkokin Afrika na MDD ya shirya a yayin cika shekaru 15 da kafa shi, a daidai lokacin babban taron mahawara na MDD game da ci gaba Afrika dake gudana a yau Alhamis.

Jerin tarurrukan wadanda suka maye gurbin makon Afrika da aka saba gudanarwa a shekarun baya, za su mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi tsaro, zaman lafiya, kare hakkin dan adam, samar da ayyukan jin kai da kuma bunkasa ci gaban nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China