in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi tir da kisan jami'in wanzar da zaman lafiya a CAR
2018-08-25 15:41:32 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da kisan jami'in wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wato CAR.

An zargin mayakan kungiyar 'yan tawaye na Anti-Balaka da kashe sojan 'dan kasar Burundi dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, ta ruwaito Antonio Guterres na jajantawa iyalan marigayin da kuma gwamnatin kasar Burundi.

Sakatare Janar din ya kara da cewa, hari kan jami'an majalisar masu aikin wanzar da zaman lafiya ka iya zama laifin yaki da kan janyo sanyawa masu hannu takunkumi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China