in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita takunkumin da ya kakabawa CAR
2018-01-31 10:10:44 cri

A jiya Talata kwamitin tsaron MDD ya sake tsawaita wa'adin takunkumin da ya kakabawa jamhuriyar Afrika ta Tsakiya (CAR), zuwa karin shekara guda, inda zai kare a ranar 31 ga watan Janairun 2019.

Mambobin kwamitin 15 sun amince da dukkan kuri'un, inda aka zartas da kuduri mai lambar 2399 don tsawaita wa'adin karin shekara guda na takunkumin hana shigar da makamai kasar.

Shi dai wannan kuduri ya amince cewa, dukkan kasashen mambobin MDD za su ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace wajen hana shigarwa, da sayar da makamai, ko yin musayar su, da sauran kayayyakin dake da nasaba da makaman a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, matakin ya hada da duk wasu makamai ko alburusai, da motocin sojoji da kayan aikin soji, da ba da tallafin kwararru, da kayan gyara, da ba da horo, da kudaden ko kuma samar da duk wani taimako da ya shafi ayyukan sojoji.

Haka zalika an tsawaita haramcin shekara guda na hana zirga-zirgar mutanen dake da alhakin haddasa rashin zaman lafiyar kasar, da kuma rufe asusun ajiyar kududen su wadanda kwamitin ya amince suna da hannu wajen haifar da tashin hankalin.

Kudurin dai ya bukaci kasashen mambobin MDD da su hana shigar dukkan mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne wadanda kwamitin MDD ya amince da zargin da ake yi musu.

Kwamitin tsaron MDD shi ma ya bukaci gwamnatin CAR da ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen musayar bayanai, kuma ta yi hadin gwiwa da kasa da kasa kan wannan batu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China