in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan sanda 7 a birnin Abuja
2018-07-04 09:31:23 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da rasuwar jami'an ta 7, sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai musu a jiya Talata, a birnin Abuja, fadar mulkin kasar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar Jimoh Moshood, ya ce tuni aka fara gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka aikata wannan ta'asa, da ma dalilin aikata hakan.

Rahotanni na cewa, an hallaka 'yan sandan ne a kan wani sha tale tale dake unguwar Galadimawa, yayin da suke aikin binciken ababen hawa.

Jimoh Moshood ya kara da cewa, ba gaskiya ba ne, zargin da wasu ke yi cewa, an harbe 'yan sandan ne a matsayin wani mataki na nuna adawa da rundunar yaki da miyagun laifuka ta 'yan sandan kasar, wadda aka fi sani da SARS.

Wasu rahotanni dai sun ce, an kara yawan 'yan sanda dake sintiri a unguwar ne, sakamakon kiraye kiraye da rundunar ke ta samu daga mazauna yankin, game da rashi tsaro, da yawan fashi da makami dake addabar su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China