in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya jaddada muhimmancin tabbatar da 'yancin dan adam na samar da abinci
2018-10-16 10:48:41 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres a jiya Litinin ya jaddada muhimmancin sabunta ayyukan tabbatar da muhimmin hakkin dan adam na samar da abinci a yayin gudanar da ranar abinci da kasa da kasa ta wannan shekara.

"A cikin wannan duniyar tamu mai cike da wadata, mutum guda cikin mutane 9 ba su da isasshen abincin da za su ci. Kimanin mutane miliyan 820 a duniya har yanzu suna fama da matsalar yunwa. Galibinsu mata ne," Guterres ya bayyana hakan cikin sakonsa na ranar abinci ta duniya.

Bugu da kari, ya kara da cewa, kimanin kananan yara miliyan 155 ne suke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, lamarin da ka iya jefa rayuwarsu cikin matsanancin hali, kana matsalar yunwa ita ce ke haddasa kashi 50 bisa 100 na yawan mace macen kananan yara a duniya baki daya.

"Kawar da yunwa baki daya ya dogara ne kan ayyukan hadin gwiwa. Kasashen duniya da kamfanoni, da cibiyoyi da daidaikun mutane: dole ne kowanne daga cikinmu ya sauke nauyin dake bisa wuyansa wajen gina ingantaccen tsarin da zai samar da wadataccen abinci ga bil adama," in ji Guterres.

Ana gudanar da bikin ranar abinci ta duniya ne a ranar 16 ga watan Oktoban kowace shekara domin tunawa da kafuwar kungiyar abinci da aikin gona ta MDD, wato FAO tun a shekarar 1945. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China