in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton WFP ya ce yake-yake na kara yawan kudin da ake kashewa ga tallafin abinci
2017-07-21 10:54:36 cri

Sabon rahoton shirin samar da abinci na duniya WFP ya bayyana cewa, tallafin abinci na ceto rayuka a lokacin rikice-rikice yayin da yake kawo karshen matsalar yunwa tun daga tushe, sai dai ya yi gargadin cewa, rikice-rikice da yake-yake na kara haifar da tsadar ba da tallafin abincin.

Rahoton ya kuma alakanta yawan kudin da ake kashewa a lokacin da ake kokarin kai agaji, da rashin samun kyakkyawar hanyar isar kayayyakin jin kai, da rashin ingataccen tsarin samar da abinci, baya ga wasu tarin matsaloli dake bukatar agajin gaggawa a fadin duniya.

Shugaban sashen dake kula da tsarin samar da abinci na shirin WFP Steven Omamo, ya ce tallafin da suke badawa ya kunshi samar da abinci mai gina jiki a lokuta da wurare da kuma yanayin da suka dace, sai dai matsalolin da dan Adam kan haifar, na kawo nakasu ga yunkurin ciyar da al'ummar duniya.

A nasa bangaren, daraktan zartarwa na WFP David Beasley, ya ce ya kamata jama'ar duniya su farka, su kuma himmantu wajen kawo karshen rikice-rikice da yake-yake, domin a samu nasarar kawo karshen yunwa.

Ya kara da cewa, kusan mutane miliyan 800, 1 cikin kowane mutum 9 ne ke kwana da yunwa, amma kuma, matsalolin da dan Adam kan haifar, na sanya taimakon wadannan mutane zama abu mai wahala matuka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China