in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin bam ya halaka mutane 6 a Mogadishu
2018-09-10 20:10:16 cri

Kafofin jami'an tsaro da na kiwon lafiya a kasar Somaliya na cewa, a kalla mutane shida ne suka game da ajalinsu, kana wasu 16 kuma suka jikkata, sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai hedkwatar gundumar Hodan a Mogadishu.

Jami'in 'yan sandan Abukar Mohamed ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dan kunar bakin waken ya kutsa da motar cikin hedkwatar gundumar Hodan, inda ya kashe mutane a kalla shida.

Darektan ayyukan ba da agajin gaggawa Abdikadir Abdirrahman ya shaidawa Xinhua cewa, a kalla mutane 16 ne aka garzaya da su asibiti. Yayin da shaidun gani da ido suka bayyana cewa fashewar ta yi barna.

Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab ta dauki nauyin kai harin na baya-bayan nan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China