in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar musamman a Somaliya ta kame wasu sansanonin al-Shabaab dake kudancin kasar
2018-08-08 09:21:19 cri

A jiya ne wata rundunar musamman ta kasar Somaliya, mai suna Danab dake samun goyon bayan dakarun kungiyar tarayyar Afirka ta kaddamar da hari kan cibiyoyin mayakan al-Shabaab, inda ta yi nasarar kwace a kalla kauyuka hudu dake yammacin garin Balad na yankin tsakiyar Shabelle dake kudancin kasar.

Kwamishin gundumar Balad Nuur Shueb, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar cewa, dakarun kawancen sun yi nasarar kwace kauyuka da dama, da a baya mayakan suka shafe watanni suna cin karensu ba babbaka.

Kauyukan da dakarun suka kwace, a cewar Shueb, sun hada da Bulo-Konto, da Dangiga Balow, da Basro da kuma Garas-weyne, dukkansu a yankin tsakiyar Shabelle.

Ya ce, sai da mayakan suka nuna turjiya inda suka yi musayar wuta da manyan makamai da dakarun kawancen kafin daga bisani su bar yankin.

Jami'in ya ce, yanzu haka dakarun gwamnati ne ke rike da yankuna hudun da suka shafe watanni da dama a hannun mayakan na al-Shabaab, sun kuma lashi takwabin fadada matakan soja zuwa Basra. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China