Kasar Sin za ta taimaka ga karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe membobin kungiyar SCO
Mai magana da yawu ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa za ta yi kokari tare da sauran kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai ko kuma SCO a takaice, domin tabbatar da nasarorin da aka samu a wajen taron kolin da aka gudanar a kwanan baya a birnin Qingdao, da kara fadada hadin-gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su samu makoma mai haske.
A 'yan kwanakin baya ne dai aka rufe taron kolin kungiyar SCO a birnin Qingdao. Yayin da yake amsa tambayoyi game da taron, Mista Geng ya jaddada cewa, taron ya saka wasu sabbin abubuwan zamani a cikin Ruhin Shanghai, da kuma kafa sabon burin da kungiyar SCO ke kokarin cimmawa, gami da sabuwar alkibla ga hadin-gwiwar kasashe membobin kungiyar.(Murtala Zhang)