in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labarai na mambobin SCO na mai da hankali sosai kan jawabin shugaba Xi Jinping
2018-06-12 10:16:50 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin taron majalisar shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 18 da ya gudana a ranar 10 ga wannan wata, jawabin da ya kara kwarin gwiwa matuka wajen kafa tsarin raya SCO bai daya. Haka kuma, kafofin yada labarai na kasashe mambobin kungiyar sun dora muhimmancin matuka kan jawabin.

Gidan telibijin na kasar Rasha NTV ya ba da labari cewa, taron ya samu ci gaba mai armashi, matakin da ya bayyana sulhuntawa da hadin gwiwa mai kyau tsakanin mambobin SCO, kuma sun samar da tafarki mai kyau ga bunkasuwar wannan yanki mai wadata.

Kafar yada labarai ta kasar Tajikistan Avesto ta ce, kungiyar SCO na dukufa kan yaki da ta'addanci, kawo baraka da tsattsauran ra'ayi, tare kuma da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Babban jigo nan taron shi ne na dunkulewar kasashen duniya masu niyyar wanzar da zaman lafiya a duniya, ya jawo hankalin karin kasashen duniya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China