Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da kakkausar murya, kan harin da aka kai wani kauyen jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya, al'amarin da ya rutsa da mutane da dama.
Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar a jiya, ta ruwaito Antonio Guterres na yin kira da a gaggauta hukunta maharan.
Sakatare Janar din, ya kuma bayyana damuwa game da yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula, yana mai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki su yi aiki tare, don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Sanarwar ta kuma ruwaito shi yana jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su da kuma gwamnati da al'ummar Najeriya, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin sauri.
A ranar Asabar ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kauyen Gwaska na jihar Kadunan Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)