in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OCHA ya yi gargadi yiwuwar fuskantar karancin abinci a arewa maso gabashin Najeriya
2016-04-28 09:27:40 cri

Ofishin MDD mai kula da al'amurran jin kai OCHA, ya yi gargadi game da yiwuwar fuskantar mummunan matsalar karancin abinci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin MDD Stephane Dujarric ya rabawa manema labaru a Larabar da ta gabata, ya ce, bincike na baya bayan nan da MDD ta gudanar ya nuna cewa, sama da mutane rabin miliyan ne ke cikin matsananciyar bukatar tallafin abinci, sannan a kalla kananan yara dubu 350 a jihohin Borno da Yobe ne ke cikin matsanacin halin karancin abinci mai gina jiki.

Tun a farkon wannan shekara, an samu damar raba tallafin abinci ga mutane sama da dubu 312, sannan an baiwa mutane 180,000 kariya, yayin da aka samar wa mutane 317,000 ruwan sha da tallafin tsabtar muhalli a kasar ta Najeriya.

OCHA ya kara da cewa, adadin kayayyakin jin kan da ake bukata a Najeriya cikin wannan shekara ya kai na dalar Amurka miliyan 248, amma aka samar da kashi 14 cikin 100 na kudaden da ake bukata ne kawai..

A yankin na arewa maso gabashin Najeriyar, manoma sun kauracewa wuraren zaman su sakamakon hare haren Boko Haram.

A kalla mutane dubu 17 ne aka ba da rahoton mutuwarsu tun bayan barkewar rikicin Boko Haram a shekarar 2009, galibinsu daga jihar Borno, sannan mutane miliyan 2 da dubu 600 sun kauracewa muhallansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China