Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba cewa, Najeriya tana fuskantar matsalar jin kai mafi muni a nahiyar Afirka, inda wasu alkaluman hukumar ke gargadin cewa, kimanin kananan yara 400,000 ne a kasar su ke fuskantar matsananciyar yunwa.
Mai rikon mukamin mukaddashin jami'in kula da harkokin jin kai na MDD Peter Lundberg ya baiwa mahukuntan Najeriya tabbacin kudurin al'ummomin kasa da kasa na yin aiki kafada da kafada da gwamnatocin tarayya da na jihohin kasar a kokarin ganin an magance wannan matsala.
Galibin mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriyar dai suna fama da matsalar tsaro, karancin abinci da kuma rashin ruwa mai tsafta.
Jami'in na OCHA ya kuma yi maraba da sanarwar baya-bayan ta kafa wata tawagar ministoci da kungiyar samar da kayayyakin jin kai da aka yi a yankin. Ya ce, yana fatan ganin ci gaba mai armashi cikin 'yan makonni ko watanni masu zuwa.
A cewarsa, duk da matsalar tsaro da wahalar kaiwa ga wasu yankunan sassan arewa maso gabashin kasar, gwamnati da sauran al'ummomi suna samarwa miliyoyin mutane da ke matukar bukatar taimako kayan agaji.(Ibrahim)