in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 12 a wani hari a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya
2018-09-09 15:39:56 cri

A kalla mutane 12 aka hallaka, kana an jikkata wasu da dama a sanadiyyar wani hari da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kaddamar a garin Gudumbali dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, wata majiyar cikin gida ce ta sanar da rahoton a jiya Asabar.

Wani mazaunin yankin da aka bayyana shi da suna Abubakar ya ce, maharan sanye da kayan sojoji sun afkawa garin, suna haye a kan babura a ranar Juma'a, inda suka bude wuta, suna harbin kan mai tsautsayi.

Abubakar ya ce, wasu daga cikin maharan sun harba makamai, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wasu mazauna yankin, mafi yawan mazaunan kananan manoma ne, wadanda suka tsere daga gidajensu.

Dubban mazauna yankin ba su jima da dawowa garin na Gudumbali ba, wanda ke da tazarar kilomita 209 daga birnin Maiduguri, babban birnin jihar, a watan Yuni bayan wani mummunan harin da aka kaddamar ya yi sanadiyyar tserewar mazauna garin kusan shekaru 3 ke nan da suka gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Texas Chukwu bai amsa kira ko kuma mayar da martani kan rubutaccen sakon da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya tura masa don neman karin bayani game da harin na ranar Juma'a ba, sai dai wata majiyar sojojin ta tabbatar da cewa, tuni hukumomi suka kaddamar da bincike kan lamarin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China