in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane 10 a Nijeriya
2018-09-05 09:25:08 cri

Gwamnatin jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 10 cikin makon da ya gabata.

Kakakin gwamnatin jihar Abubakar Dakingari, ya ce ambaliyar da ta fara a ranar Alhamis da ta gabata, ta auku ne a yankuna biyu na jihar da suka hada da Danko Wasagu da Fakai.

Kakakin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wani soja dake kokarin ceto wata mata na daga cikin wadanda suka mutu, sai dai yayin da aka gano gawar matar, kawo yanzu ba a ga ta sojar ba saboda ruwa ya tafi da ita.

Sama da gidaje 48 da gonaki da dabbobi ne ambaliyar ta lalata a yankunan biyu.

Ambaliyar ta auku ne sanadiyyar ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a jihar Kebbi, dake iyaka da garin Dosso na Jamhuriyar Nijer. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China