in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin saman Najeriya sun tarwatsa sansanin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar
2018-09-09 15:22:27 cri

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta tarwatsa kayayyakin hada boma bomai na mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a sansaninsu dake Sambisa a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Dakarun sojojin suna ci gaba da yin lugudan wuta ta sama kan mayakan, sun fara kaddamar da hare haren na musamman ne tun daga ranar 3 ga watan nan na Satumba, kamar yadda kakakin na NAF Ibikunle Daramola ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Kakakin ya kara da cewa, sojojin saman sun lalata wajen ajiye alburusai na mayakan Boko Haram a yankin Kusuma dake kan iyakar jihar Borno da tafkin Chadi.

A cewarsa, tsarin da ake bi wajen kaddamar da harin ya shafi wasu dabaru na musamman da ake amfani da su wajen lalata kayayyakin mayakan da kuma murkushe 'yan ta'addan.

Ya ce, wasu tsirarun 'yan ta'addan da suka tsira, an gano su suna tserewa daga yankin, inda wani jirgin saman yaki na sojoji ke kaddamar da hari kan mayakan ta sama.

Daramola ya ce, an fara kaddamar da hare hare a yankin na Kusuma ne, bayan samun wasu bayanan sirri dake nuna cewa akwai alburusai da wasu kayayyakin aiki mallakar mayakan na Boko Haram dake jibge a yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China