in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba abokiyar gaban Amurka ba ce
2018-10-09 19:52:27 cri

Kwanan baya mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya bayar da wani jawabi, inda ya zargi manufofin gwamnatin kasar Sin, lamarin da ya lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka, a don haka gwamnatin kasar Sin ta suki wannan jawabin, kuma ta bayyana cewa, zargin da Pence ya yi ba shi da tushe ko kadan, haka kuma tsoffin sakatarorin harkokin wajen Amurka su ma ba su yarda da ra'ayin da Pence ya gabatar ba, misali Colin Powell da Madeleine Albright, yayin da suke zantawa da jagoran shirin telibijin na CNN Fareed Zakaria a kwanan baya, sun bayyana cewa, kasar Sin ba abokiyar gabar kasar Amurka ba ce, bai kamata ba Amurka ta rika yin cacar baki da Sin.

Albright ta yi nuni da cewa, ko shakka babu kasar Sin babbar kasa ce wadda ke samun ci gaba cikin sauri, dalilin da ya sa haka shi ne domin dogon tarihin da take da shi da kuma kwazon da al'ummun kasar suke nunawa, kana Amurka ba ta yi abubuwan da suka dace a harkokin kasa da kasa yadda ya kamata, wannan ya sa kasar Sin ta samu karin damammaki na bunkasuwa.

Powell shi ma ya nuna cewa, ci gaban kasar Sin ya kawo moriya ga Amurka, kayayyakin da kasar Sin ke samarwa suna da inganci da kuma araha, haka kuma sun biya bukatun al'ummun kasar ta Amurka. Yanzu Amurka ta tada rikicin cinikayya da kasar Sin, rikicin da ya gurgunta moriyar masu sayayya na Amurka. Yana ganin cewa, gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace kan kasar Sin ba, ma'aikatar tsaron kasar ita ma tana mayar da kasashen Sin da Rasha da sauransu a matsayin abokan gaban ta, kan wannan, Powell yana ganin cewa, bai kamata ba Amurka ta yi haka, dole ne ta yi kokarin lalubo wata dabarar yin cudanya da sauran kasashen duniya, kuma wajibi ne Amurka ta yarda cewa, akwai banbanci tsakanin Amurka da sauran kasashen duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China