in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na Amurka
2018-10-08 19:08:58 cri

A yau Litinin ne, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su bi turbar moriyar juna da ta dace, maimakon tashin hankali ko yin fito na fito.

Wang Yi wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da takwaransa na Amurka Mike Pompoe a nan birnin Beijing, ya ce Pompeo ne ya shirya kawo kasar Sin kuma bangaren kasar Sin a shirye yake ya tsara wannan ganawa.

A kwanakin baya ne kasar Amurka ta tayar da rikicin cinikayya da kasar Sin, inda ta dauki matakan da suka yiwa muradun kasar Sin illa kan batun yankin Taiwan, sannan ta yi Allah wadai da manufofin cikin gida da ma na ketare na kasar Sin.

Wang Yi ya jaddada cewa, matakan da Amurka ta dauka sun yi matukar tasiri kan yadda amincin dake tsakanin bangarorin biyu ta kuma raunata makomar alakar dake tsakaninsu. Don haka jami'in na kasar Sin ya bukaci Amurka da ta hanzarta dakatar da munanan kalaman da ta ke yiwa kasar Sin.

Wang ya ce, hakan ya nuna yadda manyan kasashe biyu masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD wato Sin da Amurka ya kamata su karfafa tattaunawa da hadin gwiwa a tsakaninsu ta yadda za su sauke nauyin da al'umomin kasa da kasa suka dora musu.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce ya kamata alakar bangarorin biyu ta kasance bisa gaskiya, ya kuma bayyana fatan cewa, ziyarar da sakataren harkokin wajen na Amurka ke yi a kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar manufar da ake fata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China