in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Amurka da ta daina lalata huldar dake tsakanin su
2018-10-09 18:56:21 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Talata yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi cewa, gwamnatin kasar Sin tana fatan gwamnatin kasar Amurka za ta daina zargin kasar Sin, saboda zargin da ta yi ba shi da tushe ko kadan, kana tana fatan gwamnatin Amurka za ta daina tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, haka kuma ta daina lalata huldar dake tsakaninta da kasar Sin.

A yayin wani jawabi da ya gabatar a kwanan baya, shugaban Amurka ya zargi kasar Sin ta tsoma baki a cikin harkokin gidan Amurka da ma babban zaben kasar, Lu Kang ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin ta nace ga ka'idar rashin tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, kana ba ta shiga harkokin gidan Amurka da ma babban zaben kasar, kana a bayyane gwamnatin Amurka ta tada rikicin cinikayya tsakaninta da kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta mayar da martani ne kawai domin ta kare muradunta.

Lu Kang ya kara da cewa, hakika kasashen duniya sun gano cewa, kasar Amurka take tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, a don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina zargin kasar Sin kamar yadda take so, tare kuma da daina gurgunta huldar dake tsakaninta da kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China