in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Japan ta dauki kofin matasa 'yan kasa da shekaru 16 bayan ta doke Tajikistan da ci 1 da nema
2018-10-11 18:50:58 cri
Kungiyar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 16 ta kasar Japan, ta lashe kofin yankin Asiya na bana, bayan da ta doke takwararta ta Tajikistan da ci daya da nema, a wasan karshe da suka buga a ranar Lahadi, a filin wasa na Bukit Jalil dake birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Dan wasan gaban Japan mai lamba 10 Jun Nishikawa, shi ne ya jefa kwallon da ta baiwa kasar sa nasara, a wasan na karshe cikin minti na 63. Wannan ne kuma karo na 3 da Japan din ta dauki wannan kofi, bayan ta dauke shi a shekarun 1994 da 2006.

Tun farkon wasan dai Japan din ce ta mamaye shi, duk da ruwan sama da aka yi ta zubawa a ranar, amma su ma 'yan wasan Tajikistan sun taka rawar gani, inda suka yi iya kokarin kare hare haren 'yan wasan Japan. A minti na 58 ne kuma Japan ta jefa kwallo a ragar abokiyar karawarta, amma alkalin wasan ya ce an yi satar gida.

Kungiyoyin biyu dai sun hadu a gasar a zagaye na farko, suka kuma tashi kunnen doki maras ci. Shi ne kuma wasa daya tilo da Japan ta gaza jefa kwallo a ragar abokiyar karawar ta. Cikin wasanin da Japan din ta buga, ta samu nasara a kan takwararta ta Australia da ci 3 da 1, a wasan kusa da na kusan karshe.

A nata bangaren, duk da rashin nasarar lashe kofin gasar, Tajikistan ta yi rawar gani, duba da cewa a wasan su da mai masaukin bakin gasar wato kasar Malaysia, ta doke Malaysia da ci 6 da 2, duk da cewa Malaysia ce ta fara zura mata kwallaye biyu a wasan su na bude gasar, amma ta farke ta kuma karawa Malaysia har kwallaye hudu. Har ila ,yau ta samu nasara kan koriya ta arewa, da koriya ta kudu, a wasan kusa da kusan na karshe, da kuma wasan kusa da na karshe.

Kungiyoyi 16 ne dai suka shiga gasar ta matasa 'yan kasa da shekaru 16 ta nahiyar Asiya. Bayan kammala gasar kuma, hudu na farko za su wakilci nahiyar, a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 da za a buga a kasar Peru. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China