in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta sha alwashin doke Guinea Bissau a gasar share fagen cin kofin Afrika
2018-10-11 18:49:54 cri
Sven Vandenbroeck, babban mai horas da 'yan wasan kungiyar Zambia, ya bayyana kwarin gwaiwa na yiwuwar kungiyar zata samu nasara a wasan kwallon kafan da zata buga da takwararta ta Guinea Bissau a wasan share fagen gasar cin kofin kasashen Afrika a 2019.

Vandenbroeck, wanda yake saran za'a yi fafatawa mai zafi a gasar da za'a buga a babban filin wasa na National Heroes Stadium dake Lusaka, babban birnin kasar, yace 'yan wasan sun riga sun shirya tsab domin kafa tarihi irinsa na farko na lashe wasan share fagen.

Zambia zata kara da kasar ta yammacin Afrika ne a ranar Laraba, daga bisani kuma zata zarce zuwa Guinea Bissau don halarta karin wasannin kwanaki uku bayan wannan wasan.

"Wasanni biyun da zamu fafata da Guinea Bissau suna da muhimmanci, ba zamu yi karya game da wannan ba. Idan muka rasa maki gaba daya zamu fice ne daga gasar, da maki uku, zamu iya kare matsayin sauran sakamakon wasan," ya bayyana hakan ne a taron manema labarai gabanin gasar.

A cewarsa, Zambia tana bukatar maki daga cikin akalla wasanni biyu domin ta samu damar tsallake risadi na samun damar nasara a wasannin share fagen.

Yace ya gayyato kwararrun 'yan wasa domin baiwa Equatorial Guinea mamaki wajen taka leda da kuma nuna gamsuwa kasancewar dukkan 'yan wasansu dake zaune a kasashen ketare sun riga sun hallara a sansanin horas da 'yan wasan.

Kungiyar Chipolopolo na sahun gaba a rukunin K da maki guda tare da Namibia yayin da Equatorial Guinea da Mozambique kowannensu na da maki hudu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China