Kungiyar kwallon kafar kasar Cote d'Ivoire ta doke ta Rwanda da ci 2 da 1, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON, wanda za a yi a shekarar badi. Kungiyoyin biyu sun taka leda ne a rukuni na H, a filin kwallon Nyamirambo dake birnin Kigali a ranar Lahadi.
Kungiyar Elephants ta Cote d'Ivoire ta samu nasarar zura kwallo ta farko a ragar Rwanda cikin minti na 45, ta hannun dan wasan ta Jonathan Adjo. Sai kuma kwallo ta biyu a minti 48 ta hannun Max Alain Gradel.
Kafin a kammala wasan ne kuma Rwanda ta samu nasarar rama kwallo daya a minti 64 ta dan wasan ta Meddie Kagere, wanda ya jefa kwallo a raga da ka.
Yanzu dai Rwanda na bukatar samun nasara a wasan da za ta buga a lahadi mai zuwa, duba da cewa ta rasa nasara a wasan da ta buga a baya da janhuriyar Afirka ta tsakiya, inda suka tashi 2 da 1, a wasan da suka buga a birnin Bangui tun cikin watan Yuni na bara.
Bayan buga wadannan can wasanni, yanzu Rwandan na kasan rukunin na H, yayin da janhuriyar Afirka ta tsakiya da Guinea Conakry ke saman teburin rukunin, bayan da suka samu maki uku uku a wasannin su a zagayen farko
AFCON: Angola ta jefawa Botswana kwallo daya mai ban haushi
Kungiyar kwallon kafar kasar Angola ta doke Botswana da ci daya mai ban haushi, a wasan su na ranar Lahadi. Kungiyoyin biyu dai na yunkurin samun gurbi ne a gasar cin kofin Afirka da hukumar AFCON ke shiryawa. Dan wasan Angola Gelson Dala ne ya ciwa kasar sa kwallon daya tilo a wasan da aka buga, a filin wasan 11 de Novembro dake birnin Luanda.
Kafin hakan, a wasan da Angola ta buga cikin watan Yuni a bara da Burkina Faso, Burkina Fason ce ta samu nasara da ci 3 da 1. Duka dai a wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin na Afirka.
A mako mai zuwa Angola za ta buga wasa da Mauritania, duk da cewa Mauritania ta riga ta samu nasara kan Burkina Faso a wasan su na ranar Asabar. Ita ce kuma ta daya a rukunin.
Hukumar CAF ce ke shirya gasar cin kofin nahiyar Afirka. Ita ce kuma wadda ke lura da wasannin neman gurbi na guba wannan gasa. Za ta kuma jagoranci gasar a karo na 32, wanda za a buga a kasar Kamaru.
AFCON: Mali ta doke Sudan ta kudu da ci 3 da nema
Mali ta doke Sudan da ci 3 da nema, a yunkurin neman gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON. Wasan na ranar Lahadi dai an buga shi ne a filin wasa na Juba.
Nasarar da Mali ta samu ta sanya ta zama a saman teburin rukunin C da maki 6, yayin da Sudan ta kudu ke kasan teburin ba maki ko daya, bayan ta buga wasanni 2. A cikin shekarar da ta gabata, Burundi ta doke Sudan ta kudu da ci 3 da nema a wasan su na zagayen farko.
A wasan na karshen mako, dan wasan Mali Moussa Marega ne ya fara jefa kwallo a zare tun kafin tafiya hutun rabin lokaci. Bayan dawowa daga hutu ne kuma cikin minti na 67 Salif Coulibaly ya kara kwallo ta biyu a zaren Sudan. Ana daf da tashi kuma Adama Traore ya ciwa kungiyar ta Mali kwallo ta 3.
Da yake tsokaci bayan tashi daga wasan, kocin kungiyar Sudan ta kudu Ahcene Ait-Abdelmalek, ya ce rashin nasara da suka kwasa a wasan, ya biyo bayan karancin shiri da suka yi. Ahcene Ait-Abdelmalek ya ce sa'a ma suka yi da yake kwallo 3 kacal aka jefa masu a raga. Duba da yadda 'yan wasan Mali suka nuna kwarewa da shiri na musamman gabanin wasan. Sai dai duk da haka ya yi fatan za su samu nasara a ragowar wasannin su guda 4 na gaba, tare da Gabon, da Burundi da kuma Mali. (Saminu Alhassan)