Duk da cewa akwai dan wasansu guda dake kwance a asibiti, Kenya ta baiwa Ghana mamaki a wasan mai cike da tarihi kuma sun nuna kyakkyawar fata na samun nasara a karshen wasan.
Habasha zata taka leda da Saliyo a ranar Lahadi a Addis Ababa, Kenya tana bukatar samun nasara a wasanninta da suka rage bayan data rasa wasanta na farko da ci 2-1 a birnin Freetown a watan Yunin bara.
"Sakamakon wasan yana da ban haushi amma haka kwallon kafa ta gada. Babu wani da zai iya cika baki a harkar wasan kwallon kafa, kowace kungiya zata iya yin galaba a wasa kuma Kenya ta tabbatar da hakan," inji Atsu kamar yadda ya bayyana a ranar Lahadi a Nairobi.
"Kenya ta yi amfani da damar data samu kuma taci wasanta. Sun tsaya a baya kuma sun tsare gidansu yadda ya kamata, musamman yayin da suke da 'yan wasa 10. Sun cancanci samun nasara. Ghana ta samu damammaki amma bata yi amfani dasu ba."
Sai dai kuma, kociyan Kenya Sebastian Migne yayi gargadi game da barazanar da za'a iya samu nan gaba duk da galabar da suka samu akan Ghana.
"Har yanzu muna da matukar tazara na samun zakara don lashe gasar. Dole muna bukatar zage damtse domin mu samu nasarori akan abokan karawarmu. Bamu da kyakkyawan shiri kuma a wani tunani na shirme da wasu daga cikin 'yan wasanmu suke dashi. Amma ga wadanda suka taka leda a wasan, ina matukar alfahari dasu."(Ahmad Fagam)