180830-wasanni.m4a
|
To dai kuma daukar wannan mataki ya jefa yankin da hukumar ta CECAFA cikin wani yanayi na damuwa, kasancewar saura watanni 3 a fara gudanar da gasar.
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Kenya Nick Mwendwa, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua da wannan mataki a ranar Talata. Mwendwa ya ce Kenya ta samu damar karbar bakuncin gasar ne a bara, lokacin da kungiyar Harambee Stars ta kasar ta doke ta Zanzibar a bugun daga kai sai mai tsaron gida. To sai dai kuma sauke wannan nauyi zai gagara saboda larurar karancin kudade.
Kasashen yankin 11 ne dai aka tsara za su buga gasar ta bana. Karkashin jagorancin Kenya da CECAFA za a taka leda a gasar ajin kwararru mafi dadewa a yankin. A wannan karo kasashe da yankuna da suka hada da Zanzibar, da Tanzania, da Uganda, da Rwanda, da Burundi, da Habasha, da Eritrea, da Djibouti, da Sudan da kuma Sudan ta kudu ne ake sa ran za su kece raini.
A bangaren sa, babban sakataren hukumar CECAFA Nicholas Musonye ya bayyana takaicin sa game da matakin da Kenya ta dauka. Jami'in wanda ya yi wannan tsokaci a birnin Nairobi ya ce hakan wani kafar ungulu ni ga wannan gasa. Ya ce a ra'ayin sa akwai masu son ganin bayan hukumar ta hanyar kassara ayyukan ta.(Saminu Alhassan)