"Bayan amincewa da sakamakon zaben da babbar kotun tarayyar kasar ta yi, ina kira ga shugaban kasa da ya gayyaci wakilan majalisar domin su gudanar da zamansu ba tare da bata lokaci ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasarmu ya tanada domin fara shirye-shiryen zabar shugabannin majalisar da kuma sabon shugaban kasar," in ji Abadi a lokacin da yake jawabi kai tsaye ta gidan talabijin din kasar.
Abadi ya kuma bukaci jam'iyyun siyasar kasar dasu amince da tattaunawar mataki na gaba na kafa gwamnatin kasar, tsarin dake bukatar dukkan 'yan kasar ta Iraqi su shiga a dama dasu.
Abadi yana fuskantar matsin lamba a cikin 'yan watannin nan yayin da fararen hular kasar suka fara yin zanga zanga a yankin kudancin kasar dake lardin Basra mai arzikin mai, da wasu biranen da dama dake fadin kasar Iraqin.
Masu zanga zangar suna zargin masu fada aji a harkokin siyasar kasar da laifin fadada ayyukan rashawa wanda hakan yayi sanadiyyar karuwar rashin ayyukan yi da gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalar karancin wutar lantarkin a kasar, da ruwan sha da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa.