in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a girmama 'yancin kan Iraqi bayan harin da Iran ta kai yankin Kurdistan
2018-09-10 10:31:30 cri
Shirin MDD dake taimakawa Iraqi, ya bukaci gwamnatin Iran ta girmama 'yancin kan Iraqi.

A wani jawabi da aka wallafa a shafinsa na tweeter, shirin UNAMI ya lura da sanarwar da gwamnatin Iraqi da ta yankin Kurdawa suka fitar game da harin roka da aka kai kusa da garin Kwisanjag na yankin Kurdistan mai kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai.

Jawabin na zuwa ne kwana guda bayan Iran ta kaddamar da wani harin roka da na jirgi mara matuki kan sansanonin jam'iyyun adawa biyu na anti-Iran Kurdistan Democratic Party da Democratic Party of Iranian Kurdistan, wadanda ke kusa da garin Kwisanjag mai nisan kilomita 30 daga kan iyakar Iraqi da Iran.

A cewar majiyoyi daga asibitin garin, harin ya yi sanadin mutuwar mutane 14 da raunata wasu 39, inda 10 daga cikinsu ke cikin matsanancin hali.

Da farko, Ministan harkokin wajen Iraqi ya yi tir da harin da aka kai kan jam'iyyun adawar biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China