in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Amurka da ta yi hangen nesa kan huldar diplomasiya tsakanin Sin da Salvador
2018-08-24 19:10:38 cri

Kwanan baya fadar White House ta kasar Amurka ta fitar da wata sanarwa, inda gwamnatin kasar ta nuna damuwa kan kasar ta Salvador, saboda ta yanke huldar diplomasiya da yankin Taiwan na kasar Sin, kuma ta kulla huldar diplomasiya da kasar Sin, kana ta bayyana cewa, matakin da Salvador ta dauka ba ma kawai zai kawo tasiri ga ita kanta ba, har ma hakan zai kawo illa ga ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankali a nahiyar Amurka.

A yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya mayar da martani kan batun, kuma ya bukaci gwamnatin Amurka da ta yi hangen nesa, kan huldar diplomasiyar da kasashen Sin da Salvador suka kulla.

Jami'in ya yi nuni da cewa, Salvador ta amince da ka'idar kasar Sin daya tak a duniya, kamar yadda MDD da sauran kasashen duniya 177 suka amince da haka, kaza lika ta kulla huldar diplomasiya da kasar Sin, lamarin da ya dace da yanayin da ake ciki yanzu, kuma ya dace da dokokin kasa da kasa, da ka'idojin huldar dake tsakanin kasa da kasa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China