in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Amurka suna damuwa game da matakin karin harajin da kasarsu ke dauka
2018-08-22 18:58:26 cri

Tun daga yau ranar 20 ga wata, ofishin wakilan cinikayyar kasar Amurka, zai kira taruka a jere na sauraron ra'ayoyin jama'a, a cikin kwanaki shida masu zuwa, game da batun kara karbar harajin kwastan kan kayayyakin kasar Sin ke shigarwa Amurka, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200.

Kamfanonin kasar Amurka, suna iya kawar da hasarar da za su yi a sanadiyyar karin harajin ta hanyoyi guda biyu, wato neman samun damar ba da tallafin gata, ko kuma shawo kan gwamnatin kasar ta daina daukar matakin karin harajin, ta kuma warware rikicin cinikayya ta hanyar yin shawarwari da gwamnatin kasar Sin, ko da yake abu ne mai wahala su samu damar ba da tallafin gata.

Hakika a yayin taron sauraron ra'ayoyin jama'a da aka gudanar a kwanakin baya, mahalarta taron kaso 90 bisa dari, sun nuna adawa ga kudurin gwamnati na karin harajin, amma gwamnatin Amurka ba ta canja ra'ayinta ba. A don haka, ba zai yiwu ra'ayin adawa da 'yan kasuwar kasar za su nuna, ya yi wani tasiri ga gwamnatin kasar ba. Sai dai kila kasar ta nace ga kudurinta na karin harajin kwastan kan kayayyakin kasar Sin da take shigarwa, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200, tun daga farkon watan Satumba dake tafe.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China