in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pompeo ya yiwa shugaban koriya ta kudu bayani game da ziyarar sa a koriya ta arewa
2018-10-08 10:12:49 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya yiwa shugaban kasar koriya ta kudu karin haske, game da ziyarar da ya kai koriya ta arewa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Heather Nauert ta fitar a jiya Lahadi, ta ce Mr. Pompeo ya ziyarci birnin Seoul na koriya ta kudu, tsakanin ranekun 7 da 8 ga watan nan na Oktoba, inda ya gana da shugaban kasar, da kuma ministan harkokin waje, ya kuma yi musu bayani game da yadda ziyarar sa a birnin Pyongyang a ranar 7 ga watan Oktoba ta kasance.

Pompeo ya ce, ya gabatarwa shugaba Kim Jong-un jagoran bangaren masu shiga tsakani na koriya ta arewa wato Mr. Biegun, ya kuma yi masa karin haske game da shirin sake tattaunawa da ake yi, tsakanin wakilan Amurka da na kasar sa.

Har ila yau ya yi masa karin bayani game da bukatar cimma nasarar kudurorin da aka ayyana, yayin ganawar shugabannin kasashen biyu, na watan Yuni a kasar Singapore. Hakan kuwa ya hada da bayani game da cikakken tsarin raba zirin koriya da makaman nukiliya, kamar yadda shugaba Kim din, da takwaransa na Amurka suka amincewa.

A wani ci gaban kuma, koriya ta arewa ta bayyana bukatar ganin Amurka ta tsaya tsayin daka, wajen cika alkawarin da ta yi, na martaba yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a matsayin sharadi na raba zirin koriya da makaman kare dangi. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China