Wani rahoton da gwamnatin kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, gaba daya adadin jarin da kasar ta zuba a kasashen ketare kai tsaye wato ODI ya zarta dala trillion 1.8 a karshen shekarar 2017, lamarin da ya baiwa kasar samun matsayi na biyu a duk duniya a fannin.
Zhang Xingfu, wani jami'in ma'aikatar cinikin kasar ya ce, "Kasar Sin ta zuba jari a kasashe da shiyyoyi 189 a duk fadin duniya, inda yawan jarin ODI nata ya kai kashi 5.9 na yawn jarin waje na duniya baki daya".
Bugu da kari, yawan jarin da kasar Sin ta zuba ya fadada daga duk fannoni, in ji rahoton.
Jarin da ta zuba a bangarori 6 ya tasamma kashi 86.3 bisa 100 na yawan jarin ODI da kasar ta zuba baki daya, wanda ya hada da bangaren bada haya da ayyukan hidima, dillanci da saye da sayarwa, samar da fasahar na'urorin zamani da fasahar sadarwa ta zamani, harkokin kudi, ma'adanai, da masana'atu.
Jarin da Sin ta zuba a kasashen Turai da Afrika ya karu da kashi 70 bisa 100 a shekarar 2017, inda ta samu sabbin alkaluma na yawan jarin wanda ya tasamma dala biliyan 18.46, in ji rahoton.
A cikin wannan wa'adin, jarin da ta zuba a kasashen dake kan hanyar ziri daya da hanya daya ya kai kashi 12 bisa 100 na yawan jarin ODI na Sin, wanda ya dara kashi 31.5 na makamancin lokacin a bara.(Ahmad Fagam)