in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malawi na fatan zama cibiyar zuba jari ta Afirka
2018-06-12 09:52:41 cri

Shugaba Peter Mutharika na kasar Malawi ya ce, kasarsa ta shirya tsaf don ganin ta ci gajiyar dukkan damammakin da Allah ya horewa mata, na zama cibiyar dake janyo masu sha'awar zuba jari ta nahiyar.

Shugaba Mutharika ya bayyana hakan ne jiya Litinin a Lilongwe, fadar mulkin kasar, yayin bikin bude dandalin zuba jarina kasar (MIF) karo na 3 da taron dandalin masu ruwa da tsaki game da hade kasashen kudancin Afirka

Ya ce, Malawi karamar kasa ce, amma babba ce a nahiyar, kana kasa ce mai albarka da mutane matalauta, don haka tana da damammaki masu dinbin yawa.

Shugaban ya ce, idan har nahiyar Afirka tana matsakaicin matsayi a fannin zuba jari a duniya, kasar Malami tana son dara wannan matsayi. Don haka kasar ta shirya don zama cibiyar zuba jari ta nahiyar Afirka.

Sama da wakilai 500 daga ciki da wajen kasar daga kimanin kasashe 30 ne suka halarci taron. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China