in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da bakin haure 600,000 ne ke Libya a halin yanzu
2018-10-07 15:38:17 cri

Hukumar kula da 'yan ci rani ta kasa da kasa (IOM) ta sanar a jiya Asabar cewa, sama da bakin haure ta barauniyar hanya 600,000 ke zaune a Libya wadanda suka fito daga kasashen duniya 41.

Kasashen 5 dake sahun gaba da yawan bakin hauren a Libya sun hada da Nijer, Masar, Chadi, Sudan da Nigeria, in ji hukumar ta IOM.

Bakin hauren suna rayuwa a Libya ne a waje mai matukar cinkoso, inda aka tsugunar da dubban 'yan ci ranin wadanda dakarun tsaron tekun Libyan suka ceto su daga gabar tekun kasar.

Hukumar IOM tana gudanar da aikin sa-kai a Libya, inda take hadin gwiwa da hukumomin kasashen da abin ya shafa, da nufin mayar da 'yan ci ranin zuwa kasashensu na asali wadanda ke gararamba a Libyan.

Libya ta kasance wata matattarar bakin haure wadanda ke neman tsallakawa zuwa Turai sakamakon tabarbarewar tsaro da tashin hankali da ya barke a kasar ta arewacin Afrika tun bayan rikicin siyasar shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin shugaban kasar Muammar Gaddafi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China