in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan Libya da jakadan MDD sun tattauna matakan kawo karshen tashin hankalin Tripoli
2018-08-30 13:12:00 cri

Firaiministan Libya dake samun goyon bayan MDD Fayez Serraj a jiya Laraba ya gana da babban jami'in sakataren MDD kan rikicin kasar Libya Ghassan Salame, domin tattaunawa game da kawo karshen tashin hankalin dake wanzuwa tsakanin dakarun sojojin kasar da kungiyoyi masu dauke da makamai a Tripoli.

Ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Libya ya sanar da cewa, jami'an sun gana ne a Tripoli, babban birnin kasar kuma sun tattauna game da ci gaban da aka samu a Tripoli, dangane da batun tsakaita bude wuta da kuma yadda MDD za ta hada gwiwa da al'ummomin kasa da kasa kan wannan batu.

Salame ya jaddada muhimmancin ba da kariya ga fararen hula, da kawar da tashin hankalin cikin gaggawa, da kuma tattaunawar tsakaita bude wuta.

Tun da farko a ranar Laraba, ofishin MDD ya yi gargadi game da matakan da sojojin suka dauka a Tripoli biyo bayan tashin hankalin da ya barke tsakanin dakarun sojojin gwamnatin da masu dauke da makamai da kuma jikkata fararen hula.

Kudancin Tripoli ya jima yana fama da tashen tashen hankula bayan barkewar tashin hankali tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen masu dauke da makamai, lamarin da kawo yanzu ya yi sanadiyyar hallaka mutane 5 da jikkata wasu 33, kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China