in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya: An maida bakin haure 124 zuwa Mali
2018-08-29 09:19:41 cri

Hukumar dake yaki da kwararar bakin haure a Libya, ta mayar da wasu bakin haure 124 zuwa gida Mali, bayan da suka amince don radin kan su a mayar da su. An dai mayar da mutanen ne gida a jiya Talata, karkashin shirin da hukumar lura da 'yan gudun hijira ta duniya IOM ke marawa baya.

Wata sanarwa da aka fitar ta ce, mayar da mutanen wani bangare ne na ayyukan sa kai da IOM ke aiwatarwa, da nufin mayar da bakin haure da suka makale a Libya zuwa yankunan su na asali.

Matsugunnan bakin haure dake kasar Libya na makare da dubban mutane, wadanda aka cafke, ko aka ceto daga teku, yayin da suke yunkurin tsallakawa zuwa Turai ta tekun Meditireniya daga sassan tekun Libya.

Libya ta zamo wani sansani na masu yunkurin shiga nahiyar Turai ta barauniyar hanya, sakamakon matsalolin tsaro, da tashe tashen hankula da suka biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China