in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun kai hari hedkwtar kamfanin mai na Libya
2018-09-10 20:47:40 cri

Rahotanni daga kasar Libya na cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari kan hedkwatar kamfanin samar da mai na kasar dake yankin Dahra a tsakiyar Tripoli, babban birnin kasar.

'Yan bindigar dai sun kutsa cikin hedkwatar kamfanin ne da manyan makamai, inda suka yi musayar wuta da jami'an tsaro, lamarin da haifar da jikkatar mutane, ciki har da wani ma'aikacin kamfanin.

Ministan cikin gidan kasar Abdassalam Ashour ya bayyana cewa, 'yan bindiga shida ne suka kai hari hedkwatar kamfanin da sanyin safiyar yau, inda suka yi amfani da manyan bindigogi da gurneti, kana suka yi garkuwa da wasu mutane.

Ya kuma tabbatar da cewa, jami'an tsaro na farautar maharani. Sai dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, ko da yake da alamun kungiyoyi masu alaka da IS ne suka kai harin, duba da yanayin hare-hare da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi suka kaddamar a baya a birnin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China