Ya ce, ya kamata a tinkari matsalar 'yan gudun hijira karkashin wani tsarin da ya shafi kasashe daban daban, da daukar matakai iri-iri don daidaita matsalar tun daga tushe. Haka kuma, ya bukaci a kalli batun da idon basira, ba tare da karkata ga wani bangare ba. (Bello Wang)