Cikin manyan kusoshin akwai António Guterres, babban sakataren MDD, wanda ya ce shawarar ta shafi hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, da kokarin daidaita tsarin da ake bi wajen raya tattalin arzikin duniya. Yayin da a nasa bangare, tsohon shugaban babban taron MDD, Miroslav Lajčák, ya ce shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta nuna ma'anar ra'ayin daidaita al'amuran duniya bisa ra'ayi guda na bangarori daban daban. (Bello Wang)